Matakai guda hudu da Zaki bi wajen inganta Ni'imar jikinki cikin sauki (Banda masu Cutar sanyi da tayi karfi).
Matakin farko zaka nemi;
- Danyen zogale cikin tafin hannu biyu.
- Kwai danye guda uku.
- Albasa katuwa daya.
- Manyan tumatir guda hudu.
A yayyanka duka kayan hadin a kada da kwai a soya da man zaitun original aci awa biyu kafin Kwanciya.
Mataki na biyu Kuma Zaki nemi;
- Gwangwanin madara peak guda daya.
- Garin kanunfari cikin babban cokalin abinci daya
A hade a juya sosai asha awa biyu kafin Kwanciya.
Mataki na uku Zaki nemi;
- Garin kubewa bushasshiya cikin babban cokalin abinci daya.
- Madara peak guda daya.
A hada a juya asha awa biyu kafin kwanciya.
Mataki na hudu Kuma Zaki nemi;
- Garin kanunfari cikin babban cokalin abinci biyar.
- Garin Girfa cikin babban cokalin abinci goma sha biyu.
- Garin marke cikin babban cokalin abinci takwas.
- Zuma original ko mazarkwaila.
Awa biyu kafin Kwanciya a tafasa teaspoon daya a saka mazarkwaila ko zuma asha.
SHARADI
- Banda masu ciki.
- Banda masu ciwon sanyi me karfi.
Comments
Post a Comment