Main menu

Pages

NASIHOHI GA DUK MUSULMIN DA YA SAMU KANSA CIJIN DAMUWA

 



Nasihohi guda Tara ga duk Wani Musulmi da ya tsinci kansa cikin wata muguwar damuwa.


★ Ka tsaya ka binkica kanka ka duba tsakaninka da Allah, da'ar ka ga Allah, ya ya take? Ka duba kaga shin baka aikata wasu ababen da Allah ko baya so? Idan ka san  akwai matsala ka gyara.



★ Sannan alaqar ka ga iyaye ka duba kaga kana kyautata musu yanda ya kamata?sannan babu wani mutum da ka ke zalunta??



★ Idan wani abune kake tsoron faruwan sa ko yake baka tsoro Karka manta da fadin (Hasbunallahu wani'imal wakeel) "ita Annabi Ibrahim ya fad'a lokacin da aka jefashi wuta, sai wutar ta koma Sanyi mai aminci"



★ Manzon Allah ﷺ ya ce:  idan Allah Ya yi nufin bawan sa da alkhairi sai Ya jarabce shi da musiba". 

 To, kada ka damu, ta yiwu wata hanya ce da Allah Yake so Ya daukaka darajanka, ko ka gane wasu kusakuran naka ka kuma kara kusanci gareshi Allah (S W T)



★ Kada ka nemi biyan buk'atarka gurin wani mutum, kada kuma ka rika fadan yasassun maganganu akan damuwanka, ka kyautata ma Allah zato ka kame, sannan ka kame gabban ka daga Sabon Allah



★ Maida lamari ga Allah da neman taimakon sa, ka dauka, cewa duk wata damuwarka shi ne zai maka magani, dole dama rayuwa akwai jarabawa, bazaka taba jin yadda kake so ba ko yaushe, kuma duk lokacin da tsanani ya yi yawa akwai sauki yana tafe.



★ Yawan Sadaka da abinda da Allah ya hore maka mai kyau, kayi tawassili Allah ya yaye duk wata damuwa.da yawan Sallan dare (daya bisa uku na karshe) lokaci ne na Amsa addu'a



★ Yawan zikiri ambaton Allah, da suka tabbata a sunnah (duba Hisnul Muslim).

Sannan  koda kana aiki ne, bakin ka ya yawaita zikiri, da Salatin Annabi da Istigfari, da addu'ar (La'ila ha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin)..



★ Idan sauki ya zo, (lokacin da kake cikin jin dadi) kada kuma ka manta da Allah, da yawan ci gaba da Addu'a da kuma godiya gare shi a ko wani hali da kiyaye dokokin sa.



 Ya Ubangijin mu! Duk wani Wanda yake cikin kunci da jarabawa ta rayuwa Allah ka bashi ikon cinyewa Ka kawo masa sauki da mafita 

Ameen 

Comments