Ko kunsan tasiri da sirrinkan dake cikin yawaita yin lalle ga Mace?
Macen da take da ni’ima ma’ana wacce Allah ya san ya wa yawan sha’awa a jiki da kuma damshin jiki da gamsarwa, idan tana yin lalle to sha’awar da ni’imarta ba za su gushe ba har sai sanda tsufa ya kai wani mataki.
Lalle na maganin cututtukan da ke lailayi a baki kamar zubar jini a sanda ake kurkurar baki ko kuraje ga harshe ko a cikin baki na ba gaira ba dalili. Sai a tafasa ganyen lalle a dunga kurkure baki da ruwan a kalla sau uku a wuni.
A bangaren gyaran fuska, lalle ya zarce sauran kayan kwalliya domin duk yanda kike amfani da foda a fuskarki, to ba za ta kai lalle tasiri ba domin shi lalle har sha’awa yake karawa mace, haka kuma yana janyo hankalin namiji yaji yana sha’awar matarsa muddin tana yawan yin lalle.
Bayan haka lalle maganine da kuma kariya daga sihiri da sauran sharrin masu sheri, duk macen data jure yin lalle akai akai to insha Allahu zata samu kariya daga shaidanu da sihirce sihirce. Wannan kadanne daga cikin amfanin lalle insha Allahu nan gaba zamu kawo maku sauran Amfanin sa.
Comments
Post a Comment