Main menu

Pages

WANI HADIN MAGANIN ZAZZABI DA ZA A HADA CIKIN SAUKI

 



Yadda za ayi Maganin Zazzabi cikin sauki. Wani hadin Maganin Zazzabi kashi na 3.

Naga mutane nata fama da masassara a wannan lokaci saboda yanayin canjin lokaci da aka samu.


Ga Abubuwan da za'a naima Insha Allahu za'a samu waraka.


1. Kimba ta N100 

2.Kanunfari N100

3. Ɗanyar citta (Ginger) ta N100




A hada su waje guda a jajjaga su (Blending) sannan a tafasa su a tukunya, idan ya tafasa sai a sauke ayi surace. Amma kafin ayi suracen a ɗebi kofi daya a sha da zafin sa kamar shayi.

A daure a gwada.



Duk wanda yayi haka ba zai kwana da zazzabi ba, Insha Allahu, zaka iya rabawa 2, kayi sau 2.


Allah yaƙara mana lafiya

Comments