Main menu

Pages

WASU ALAMOMI GUDA 7 DA IYAYE ZASU GANE CEWA KO JARIRINSU NA TARE DA MATSALA

 



Wasu alamomi guda Bakwai (7) dake alamta cewa Jaririnku na tattare da Matsala.


Sau da yawa a shafukan sada zumunta, ko kuma a rayuwa ta yau da kullum, za ku ga yadda iyaye ke ɗoki a duk lokacin da jinjirinsu ya iya wani abu da bai taɓa yi ba, ko kuma ya kai wani mataki na rayuwa.




Kamar lokacin da ya fara dariya, ko rarrafe, ko takawa ko kuma magana, da makamantansu.

Wani bincike a Amurka ya ce kashi shidda a cikin goma na iyaye na damuwa game da yadda jariransu ke girma.




Amma wasu iyayen kuma ba su damu ba, suna ƙullawa a ransu cewar komai zai kasance a lokacinsa, kasancewar yara na girma da iya abubuwa ne a lokuta daban-daban, daidai da yanayin halittarsu.




Sai dai masana na cewa akwai wasu alamu da ya kamata iyaye su lura da su a wasu matakai na rayuwar jariri bayan haihuwa, ta yadda za su fahimci ko yaro na neman kulawa ta musamman ko kuma taimako.



A kan haka ne babban likitan yara a asibitin Nizamiye da ke Abuja, Dakta Lawal Musa Tahir, ya bayyana wasu alamomi da suka kamata iyaye su sanya ido a kansu a lokacin da jariri ya kai wata shidda da haihuwa.




- Rashin tsayawar wuya: Idan ya kasance wuyan jariri ba ya tsayawa a lokacin da aka dauke shi, misali, idan aka kwantar da shi a rigingine, sannan aka kama hannuwansa biyu aka ɗaga shi, idan a wannan lokacin ba ya iya tsayar da wuyansa, to wannan alama ce ta cewa ya kamata a kai shi wurin likita domin dubawa, a cewar dakta Attahiru.



- Rashin nuna alamar jin ƙara: Idan har jariri ɗan wata shidda, a lokacin da aka yi wata ƙara, ko tsawa, ko aka rufe ƙofa da ƙarfi “aka ga alamar bai nuna ya san an yi ƙarar ba, to akwai buƙatar a bincika a san dalili.”



- Rashin bin abu da ido: Ya kamata idan aka gitta wani abu a kusa da fuskar jariri ɗan wata shidda, ya iya bin shi da kallo, daga dama zuwa hagu, ko daga hagu zuwa dama. Amma a cewar Dr Attahiru idan har aka yi masa haka aka ga ba ya bin abin da kallo to akwai buƙatar a bincika saboda akwai alamun da ke nuna cewa akwai matsala.




- Rashin dariya: “A wata shidda ya kamata a ce idan aka yi wa jariri wasa ya rinƙa dariya sosai”, a cewar likita, ya ce idan har ba a ga hakan ba, to akwai buƙatar a duba shi.




- Rashin gane mahaifiyarsa: Ya kamata a ce jariri ɗan wata shidda ya san fuskar mahaifiyarsa, ya rinƙa gane ta, ya gane muryarta, sannan zai gane fuskoki da muryoyin wasu ƴan gidansu.




Rashin kifewa: Ya kamata jariri ɗan wata shida ya iya juyawa ya kwanta ruf-da-ciki a lokacin da aka kwantar da shi a rigingine.



- Gaza kai hannu baki: Ya kamata jariri ɗan wata shidda ya iya kai hannunsa baki, musamman a lokacin da aka miƙa masa wani abu a hannunsa.



Dakta Lawal Tahir ya ce duk da cewa akan samu banbanci a yanayin girman jiki da na ƙwaƙwalwar jarirai, ya kamata iyaye su damu, kuma su kai jariri asibiti, matuƙar aka lura da irin waɗannan almomi a tattare da shi.




Abubuwan da ke iya haifar da irin waɗannan matsaloli

Likitan ya ce akwai abubuwa da dama waɗanda ke iya haifar wa jariri irin waɗannan matsaloli, waɗanda ba za a iya tantance su ba sai da sa hannun masana ta hanyar gwaje-gwaje.



Kasancewar wasu matsalolin na samo asali ne daga ƙwayar halittar gado, ko lokacin girman ɗan-tayi a cikin mahaifa, ko kuma a lokacin haihuwa.



Haka nan ya ƙara da cewa akwai lokuttan da jariri kan samu irin waɗannan matsaloli saboda cututtuka ko yanayin da ya tsinci kansa bayan haihuwa.

Comments