Hadarin da Mata kan shiga wajen soyayyar social media da ya kamata su kiyaye shiga hadari da rudani.
Duk imaninki, duk iliminki, duk wayonki, duk tsoron Allanki namiji zai iya cin galaba akanki da taimakon shaidan ta hanyar soyayyar kafar sadarwar zamani, ki gujeshi baki daya kawai domin baki iya gane wanene zaizo da gaskiya.
Sai kin kiyaye sannan Allah zai kiyayeki.
Yar uwa ta yaya wanda bai sanki ba, bai San asalinki ba, baisan yanayin halittarki ba, yace yanas onki kuma har ki yarda?
Yar uwa Karya namiji yake, yace wai sonki yake saboda addininki ko iliminki ZALLAH batare da bukatar wasu abubuwa da yakamata ace kin mallaka don dorewar zaman aure ba.
1) Wani burinshi kawai mutane su jinjina masa cewar yayi soyayya dake, amma baya bukatar ki zama matarsa.
2) Wani kuma so yake yasamu wacce zata dinga fada masa kalaman soyayya idan yana online, dazaran yabar Facebook ya manta dake.
3) Zaki iya sallama zuciyarki ga wani sai kinyi nisa a sonsa, ya gama jin dadadan kalamanki, ya Riga yasan sirrikanki ya guduvya barki, yar uwa yaya zakiyi tunda haduwar Facebook ne? Ina zaki gano shi bayan kin kamu da sonsa??
4) Wani kuma dama karya yake ba sonki yake ba, hotonki kawai yake son samu, dama aikinsa kenan kullum tara pics din 'yan mata.(Jan kunne ga 'yammatan dake turawa samari pictures daga haduwa a social media)
5) Wani zai iya amfani da hanyoyi da zaki kamu da sonsa, wanda daga karshe zaiyi amfani da son da kike masa yajaki zuwa aikata abinda zakiyi nadamarsa har abada, abinda ke kanki zaki kasa yafewa kanki.
6) Da zarar kin fara bude zuciyarki wajen karban soyayyar wani, to akwai yiyuwar idan wani yasake zuwa ki amsa mashi, kenan kin zama YAR YAUDARA.
Don haka ya kamata Mata marasa aure su kula su hankalta da suwaye zasu yi Mu'amala dashi a social media. Sannan ba duka Mazan social media din ne suka hadu suka zama daya ba, akwai nagari a cikinsu.
Saboda komai Lalacewar zamani akwai na Allah a ciki kamar yadda a zahirance akwai samari nagari akwai na banza to haka ma a social media din. Akwai mutane da yawa da suka yi aure ta dalilin social media din Kuma har yanzu suna tare. To Dan haka sai ayi taka tsan -tsan asan da waye za ayi Mu'amala.
Comments
Post a Comment