Main menu

Pages

YADDA ZA A HADA MAGANIN CIWON HAKIN WUYA

 



Yadda za a hada Maganin ciwon Hakin wuya/ Dan wuya, ga masu fama da wannan ciwon.

Bayan ancirewa mutum hakin wuya  yakan sake tsirowa, amma hakan nafaruwa ne da mutane daidaiku. Masu fama da ciwon hajin wuya sunajin alamun kamar haka:

- Zakaga mutum yanata yawan amai,

- Kuma zaiji wani Abu ya tokare shi a makogwaro,

- Idan wani Abu yataba wajen zaiji zafi sosai, 

- Kuma zaita ramewa,




To idan mutum yashiga irin wannan halin.  Yaje adubashi Dan a tabbatar masa da cewa hakin wuya ne yasake tsirowa,


Wasu suna yarda asake yanke masu, wasu kuma sai su bukaci abasu magani.

Haka kuma akwai Wanda tun suna jarirai ba'a ciremasu shi ba (cirewan bashi da wani amfani)




Abinda yake sawa belin wuya ko hakin wuya yasake tsirowa mutum, shine in mutum yana yawan shan gishiri. Amma abinda nafiso Mutane su gane shine, shi ciwon hakin wuya, kamar sauran ciwuka ne, za a ce mutum na ciwon Ido, ko Ciwon kunne ko na Hakori. To Shima wasu na fama da ciwon hakin wuya bawai don ba a cire bane, ko ace an cire bai ciru ba ko ya sake fitowa.



Akwai maganin gargajiya da wanzamai suke bayarwa akan hakan , Maganin kuwa shine



Asamu harshen kaza daya, da gabobin karan dawa 3 da iccen kirya a hada su ajika sannan asamu karfen gatari asakashi awuta in yayi zafi sosai adaukoshi asaka cikin ruwan maganin sannan sai arika shan ruwan rabin Kofi sau 2 arana

Comments