Yadda za a Magance Matsalar Uric Acid dake Sanya ciwon gabobi da gwiwa.
Masu tambayar menene uric acid, wani sinadari ne da ake samu a cikin nau'ikan abinci ko abin sha da yake da purine a cikin sa.
Yayin da kaci wannan nau'in abu mai purine a ciki hanta ita ce ke tacewa tare da raba abinda kaci zuwa kowanne sassa, wannan purine yana fitar da uric acid.
Shi kuma uric acid Qoda ita ce take tace ahi daga jikin mutum, idan yayi yawa ko kuma Qoda bata iya tacewa yadda ya kamata zaibi hanyoyin jini ya haifar da matsala.
Kuma matsalar da yake haifarwa shine a gabobi da jijiyoyin mutum, zaka rika fama da rikewar gaba ko gwiwa.
Sannan idan yayi yawa a jini yana haifar da gout,wani kumburi ne a kafa, musamman babban yatsan mutum ya rika zafi yana ciwo.
Idan uric acid yayi yawa yana hana mutum tafiya ko tashi ko motsi yadda yake so.
Akwai masu fama da wannan matsala ta uric acid amma basu sani ba suna dauka sanyi ne.
Saboda haka a rika zuwa asibiti kafin neman magani.
Yadda za a Magance wannan matsala ta uric acid shine za a samu Ganyen magwaro a tafasa shi ana Shan Kofi daya da safe daya da yamma.
Allah yasa mu dace.
Comments
Post a Comment