Yadda Ake Hada kalolin ingantattun Tsumin Mata kala - kala har kala uku,
Ki samu ganyen xogale ki wanke ki tabbatar Babu datti sau cocumber (gurji) ki fere shi ki yanka ki hada da ganyen Zogale ki markada da blander sai ki tace ruwan ki zuba madara da Zuma aciki idan kina so yayi sanyi ki saka a firij yayi sanyi. Sai kisha.
Da farko dai zaki iya samun dabino bayan kin cire kwallon sai ki jikashi ya jiku ki zuba masa kanunfari da minannas ki markadasu ki tace ki saka Mazarkwaila bayan ta narke a ciki shikenan kingama sai ki ajiye kina sha
Ko kuma zaki iya samun ruwan kwakwa da madara peak da Zuma sai garin ridi ki hadasu guri daya ki gauraya shi sosai, ki ajiyeshi kinasha wannan ga ni'ima ga qarawa macce yawan sha'awar Mijinki.
Comments
Post a Comment