Yanda Ake Hada Sabulun Fuska da na jiki da Abubuwa masu sauki.
- Sabulun salo
- Sabulun zuma
- Zuma
- Aloevera
- Man Zaitun
- Kwakwa
A samu sabulun salo ko sabulun ghana kamar girman sabulun giv guda biyu, a samu sabulun zuma guda daya idan ba a sameshi ba a sa alorvera soap, a daka sabulun ko a goga a sa ruwan ganyen alorvera cokali uku, zuma cokali uku, man zaitun cokali daya, man kwakwa cokali daya, a hada a kwaba, a dinga shafawa a fuska, bayan minti goma ko sha biyar a wanke fuskar yana saka kyan fuska tayi shaining ta yi kyau.
Abubuwan da za a nema don hada Sabulun wanka na jiki, sune kamar haka;
- Sabulun ghana
- Majigi
- Zuma
- Lemon tsami
- Zaitun
A hada sabulun ghana da majigi a dake a zuba zuma a matsa lemon tsami kadan a saka man zaitun cokali daya a bada a kwaba, bakar mace da bata son ta yi fari sai ta dinga wanka da shi, zai sa tayi kyau, fatarta tayi taushi da santsi bakinta ya dinga kyalli
Comments
Post a Comment