Main menu

Pages

YANDA AKE HADA SABULUN FUSKA DANA DON GYARAN JIKI

 

Yanda Ake Hada Sabulun Fuska da na jiki da Abubuwa masu sauki.

Abubuwan da za a nema don hada Sabulun Fuska gasu kamar haka;

– Sabulun salo

– Sabulun zuma

– Zuma

– Aloevera

– Man Zaitun

– Kwakwa

A samu sabulun salo ko sabulun ghana kamar girman sabulun giv guda biyu, a samu sabulun zuma guda daya idan ba a sameshi ba a sa alorvera soap, a daka sabulun ko a goga a sa ruwan ganyen alorvera cokali uku, zuma cokali uku, man zaitun cokali daya, man kwakwa cokali daya, a hada a kwaba, a dinga shafawa a fuska, bayan minti goma ko sha biyar a wanke fuskar yana saka kyan fuska tayi shaining ta yi kyau.

Abubuwan da za a nema don hada Sabulun wanka na jiki, sune kamar haka;

– Sabulun ghana

– Majigi

– Zuma

– Lemon tsami

– Zaitun

 A hada sabulun ghana da majigi a dake a zuba zuma a matsa lemon tsami kadan a saka man zaitun cokali daya a bada a kwaba, bakar mace da bata son ta yi fari sai ta dinga wanka da shi, zai sa tayi kyau, fatarta tayi taushi da santsi bakinta ya dinga kyalli

Comments