Main menu

Pages

YANDA HATSARIN MOTA YA RITSA DA SANI DANJA DA SANUSI OSCAR 442

 



Yanda Hadarin Mota ya ritsa da Sani Danja da Sanusi Oscar 442 akan hanyar Abuja Zuwa Bauchi.


A yanzu nan majiyarmu ta samu wani labari marar dadi amma kuma akwai sauki a cikinsa inda manya manyan jaruman Masana’antar kannywood suka yi hadarin mota a bisa hanyar zuwa jihar Bauchi daga birnin tarayya abuja kamar yadda shafin dimokuraɗiya suka ruwaito a shsfinsa na sada zumunta facebook inda suke cewa.






Yanzu haka Jarumin masanaantar shirya fina finan hausa na Kannywood, Sani Musa Danja, yayi hatsari a kan hanyar sa daga Abuja zuwa Jihar Bauchi.





Binciken da Jaridar Dimokuradiyya tayi, ya nuna cewar a lokacin da suka yi hadarin Sani Danja yana tare da Darakta Sanusi Osca442.




Sun bar Abuja a Safiyar yau Alhamis a kokarin su na zuwa Jihar Bauchi, don halartar gangamin kaddamar da takarar Shugabancin kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP.




Rahotanni sun tabbatar da cewar lamarin ya zo cikin sauki Kuma an dauki dukkan Matakan da suka dace.



Har ila yau rahoton yace Motar da suke a ciki ta Sami damuwa sosai don ko tashi bata yi bare ayi Shawarar cigaba da tafiya.


Muna rokon Allah ya tsare gaba da sauran dukkan matafiya Allah ya kai kowa lafiya ya dawo da shi lafiya ameen.

Comments