Abubuwan dake haifar was Mai ciki yin 6ari da Kuma wasu magunguna da ke janyo barin ko kashe yaro a ciki ko nakasa shi.
Akwai matukar ciwo asami rabo na juna biyu akarshe azamto anrasa shi. Wanda bisa kididdiga a dukkan mata 4 masu ciki akalla 1 na rasa nata yayin da 3 kadai kekai labari.
Da farko akwai bambanci tsakanin 6ari wato miscarriage da kuma mutuwar yaro aciki wato stillbirth.
In ciki ya zube kasa da sati 23 na goyonsa wato watanni 5 shine ake cewa 6ari. Amma duk cikin da ya zube bayan sati 23 a Duniya ko sati 28 wannan shine mutuwar jariri wato still birth.
Abubuwa ne da sun yawaita a yanzu to amma dan gane da 6ari wato miscarriage abubuwan dake haddasawa sune;
■ Rashin lafiyar cikin mahaifar mace wato kila akwai wata nakasa ta halitta a mahaifar,
■ Sai kuma yawan zirga-zirga ace ana da yaron ciki amma arika daukar mace ko ita akaran kanta ta rika tafiye-tafiye a mota ko akasa ta sama da awa 2 da rabi, ko tafiyar babur ta kimanin minti 15 zuwa 20,
■Ko yawan aikin karfi ba hutu,
■ Sai kuma raunin ko rashin kwarin bakin mahaifa wato cervix insufficiency a wadanda keda karancin sinadarin protein din dake ba cervix din kwari wato collagen adalilin gado,
■ Sai kwayoyin cuta irinsu PID da infections din nan dake descending ya shige,
■ Sai cutukan koda (kidney disease),
■ Ciwon suga da kuma
■ Ture-turen sassake-sassake ko tsarki da abubuwa iri-iri a farji da mata suka cusa kansu ciki a yanzu, wanda wani ruwan maganin yana sa bakin mahaifar mace ya bude ne wato Dilatation
■ Sai kuma abu na karshe shan magunguna daka kuma barkatai walau na hausa ko na asibiti batare da tuntubar masana ba; kuma abunda baku sani ba cikin magungunan hadda kuwa irinsu; Ibuprofen (motrin), Cataflam, Aspirin da kukafi rainawa.
Ballantana kuma Tetracycline wanda kuka fi sani da 'Ja da yellow💊 wanda wannan maganin yana da mugun hatsari koda ciki ya zauna ana iya haifo yaro me naqasa, Sauran sune su;
Chloramphenicol, Ciprofloxacin, levofloxacin, septrin, Codeine, misoprostol da masu ulcer kesha da sauransu suna nan
Allah Ya tsare Ya sauke masu ciki Lafiya.
Comments
Post a Comment