Main menu

Pages

ABUBUWA 9 DA KE HADDASA BARI KO MUTUWAR YARO A CIKI

 

Abubuwan dake haifar was Mai ciki yin 6ari da Kuma wasu magunguna da ke janyo barin ko kashe yaro a ciki ko nakasa shi.

Akwai matukar ciwo asami rabo na juna biyu akarshe azamto anrasa shi. Wanda bisa kididdiga a dukkan mata 4 masu ciki akalla 1 na rasa nata yayin da 3 kadai kekai labari.

Da farko akwai bambanci tsakanin 6ari wato miscarriage da kuma mutuwar yaro aciki wato stillbirth. 

In ciki ya zube kasa da sati 23 na goyonsa wato watanni 5 shine ake cewa 6ari. Amma duk cikin da ya zube bayan sati 23 a Duniya ko sati 28 wannan shine mutuwar jariri wato still birth.

Abubuwa ne da sun yawaita a yanzu to amma dan gane da 6ari wato miscarriage abubuwan dake haddasawa sune; 

■ Rashin lafiyar cikin mahaifar mace wato kila akwai wata nakasa ta halitta a mahaifar, 

■ Sai kuma yawan zirga-zirga ace ana da yaron ciki amma arika daukar mace ko ita akaran kanta ta rika tafiye-tafiye a mota ko akasa ta sama da awa 2 da rabi, ko tafiyar babur ta kimanin minti 15 zuwa 20, 

■Ko yawan aikin karfi ba hutu, 

■ Sai kuma raunin ko rashin kwarin bakin mahaifa wato cervix insufficiency a wadanda keda karancin sinadarin protein din dake ba cervix din kwari wato collagen adalilin gado, 

■ Sai kwayoyin cuta irinsu PID da infections din nan dake descending ya shige, 

■ Sai cutukan koda (kidney disease), 

■ Ciwon suga da kuma 

■ Ture-turen sassake-sassake ko tsarki da abubuwa iri-iri a farji da mata suka cusa kansu ciki a yanzu, wanda wani ruwan maganin yana sa bakin mahaifar mace ya bude ne wato Dilatation 

■ Sai kuma abu na karshe shan magunguna daka kuma barkatai walau na hausa ko na asibiti batare da tuntubar masana ba; kuma abunda baku sani ba cikin magungunan hadda kuwa irinsu; Ibuprofen (motrin), Cataflam, Aspirin da kukafi rainawa.

Ballantana kuma Tetracycline wanda kuka fi sani da ‘Ja da yellow💊 wanda wannan maganin yana da mugun hatsari koda ciki ya zauna ana iya haifo yaro me naqasa, Sauran sune su;

Chloramphenicol, Ciprofloxacin, levofloxacin, septrin, Codeine, misoprostol da masu ulcer kesha da sauransu suna nan

Allah Ya tsare Ya sauke masu ciki Lafiya.

Comments