Abubuwan da ya kamata ki fara ci da Kuma sha bayan haihuwarki da Sati biyu har Zuwa Ar'ba'in.
Za ki Fara shirya jikinki don tarbar maigida, don in dai lafiya kika haihu daga lokacin zaki tsinci kanki cikin kuzari da Lafiyar jiki.
Duk wanda ya ganki zai ganki tas kamar ba ki haihu ba.
Don haka tunda tafiyar ta samu sai a Fara shirya jiki, Kiyi kokarin a dafa miki kaza irin ta masu jego ki Fara ci, ( Inda babu kada ki matsawa mijinki ) cin kazar yana Kara gyaran kasan mace maigida yaji ta zam-zam kamar bata haihu ba.
❮❯ Shan ya'yan itatuwa akai-akai baran ma ( kankana, abarba, gwada, lemon Zaki.
❮❯ Ki dinga yin Kunun aya kina sha. In zai samu Kiyi kullum, Amma karki dinga zuba sukari Dan kadan Zaki dinga sawa ko ki sha haka.
❮❯ Shan maganin Mata mai kyau ( habbatus-sauda, Zuma , dabino, aya ,madara , nono Amma me kyau.
❮❯ Shan Zuma madi, tsimi da saurabsu.
❮❯ Tun Daga ranar da kika haihu har zuwa lokacin da Zaki yi arba'in ki zama cikin tsaftace jiki da gyaran jiki, gyaran jariri ,gyaran gida.
Comments
Post a Comment