Main menu

Pages

AMFANIN KANKANA GUDA SHA BIYU GA LAFIYAR DAN ADAM

 



Kadan daga cikin anfanin kankana ajikin dan'adam, da ba Kowa ne ya sani ba.


- Kankana na dauke da sinadarin dake samar da kariya da rage barazanar cutar hawan jini ga jikin bil'adama (Hypertension)



- Kankana na taimakawa matuka wajen rage yawan kiba da nauyin jiki mai cutar da bil'adama.



- Kankana na dauke da sinadarin “Glutathione” wanda ke taimakawa wajen kwarara garkuwar jikin bil'adama.



- Kankana na dauke da sinadarin “Lycopene” wanda yake dagargaza kwayoyin cutar daji (Cancer)



- Kankana na dauke da sinadarin (Vitamin C) wanda ke da tasiri wajen kashe kwayoyin cutar da ke cikin jinin bil'adama.



- Kankana na dauke da sinadarin “Potassium” wanda ke taimaka wa zuciya, k'oda, Huhu da sauran muhimman sassan jikin bil'adama.



- Kankana na samar wa fatan bil'adama kariya daga illolin daga haske da tsananin zafin rana.


- An bayyana masu shan Kankana da wadanda cutar Asthma za ta yi wuyar kama su saboda sinadarin Vitamin C da Kankana ke da shi. (Asthma prevention)



- Kankana na taimakawa jikin bil'adama wajen narkar da abinci cikin tsari.



- Kankana na samar da kariya da rage barazanar cutar sugar ko Diabetes.



- Kankana na samar da kariya ga cutar ciwon zuciya (Heart Attack).


- Kankana taimaka wa ma’aurata da kuzari da nishadi musamman a yayin gabatar da ibadan aure.

Comments