Main menu

Pages

AMFANIN MAN HABBATUSSAUDA GUDA SHA BAKWAI (17)

 



Yanda za a sarrafa Man Habbatussauda wajen magance cututtuka guda goma Sha bakwai (17).



1- Ciwon sugar (Diabetes)

Ga masu fama da ciwon sikar sai su samu zuma mai kyau su hada da man Habbatus- Sauda a mazubi mai tsafta, sai su gauraye wannan hadin, za su sha cokali daya sau biyu a rana. Sannan yana da kyau su kauracewa shan sikari da duk wani nau’in kayan abincin da zai iya sa lalurar tayi karfi.




2 - Ciwon Daji (Cancer)

Ga mai fama da ciwon daji, sai ya samu man Habbatus-Sauda da zuma ya hada waje guda a mazubi mai tsafta. za asha cokali daya kafin a ci komai da safe, daya da rana, daya da daddare kafin a kwanta barci.




3 - Hawan Jini ( Hypertension)

Ga mai fama da hawan jini, a kullum zaka zuba rabin cokali na man Habbatus-Sauda a ruwan zafi dai dai yadda za a iya sha, bayan ya huce kadan sai a sha. Sannan a kasance masu yawan amfani da tafarnuwa, a abinci, ko shayi , motsa jiki musamman lokacin da rana ta fara fitowa kafin tayi zafi sosai.




4 - Tari; Rabin cokali na man Habbatus -Sauda za a zuba a cikin kofi daya na shayin kofi (Coffee) za a yi haka sau biyu a rana, sannan ka shafa man Habbatus-Sauda a kirjin ka da kuma gadon bayanka.



5 - Qarin Mahaifa (Fibroid); Abinda za ki yi anan shi ne ki samu man Habbatus-Sauda da zuma za ki hada awajen guda dai-dai yawan su ya zamo daya, sai ki zuba su a mazubi daya, za ki sha rabin cokali sau uku a rana.




6 - Ciwon Kai Mai Tsanani; Ga mai fama da matsalolin ciwon kai sai ya samu man Habbatus-Sauda ya shafa a gaban goshin sa, sannan ya dan diga kadan a hanci, baya ga haka ya kasance mai cin irin habbatus-Sauda bayan an gasa shi kadan tare da zuma, akalla sau biyu a kowace rana.



7 - Mura da Sanyi; Ga mai fama da mura sai ya samu zuma su hada da Man Habbatus-Sauda, sai ya sha rabin cokali a kullum sannan su diga man kadan a cikin hanci.




8 -Tsiro akan Fata; Abinda za ka yi , shi ne sai ka nika irin kwayar Habbatus- sauda , sai ka kwaba da ruwa, sannan ka shafa akan wannan tsiron. Sau biyu a rana.




9 - Matsalolin da suka shafi Hancu da Makogwaro. 

Ga mai fama da irin wannan matsalolin, sai ya samu lemun tsami mai kyau, ya matse ruwan a kofi sannan ya zuba ruwan zafi sosai akai, rabin cokali na man habbatus- Sauda, sannan sai ya shaki wannan tiririn ruwan zafin. Haka zai yi sau biyu a rana.




10 - Inganta Lafiyar Fata

Habbatus- Sauda za ki samu sai ki hada da man zaitun, sai ki wanke fuskar, wannan hadin za ki shafa a fuska, bayan awa daya sai ki wanke.



 11 - Zubar Gashin Kai

Ga mata masu fama da matsalar zubewar gashi, sai su hada man Habbatus_Sauda da man Zaitun, bayan su tsefe gashin sai su bi layi-layi na gashin suna sa masa man tare da yiwa kan tausa. 




12 - Ciwon Kunne; Irin kwayar Habbatus-Sauda za ka gasa shi sama-sama, sannan ka ni ka shi , sai ka sa man Habbatus- sauda rabin cokali, man Zaitun rabin cokali, sai ka hadesu a mazubi mai kyau, sirinji zaka samu sai ka dure wannan hadin maganai aciki, zaka diga akunne sau biyu a rana.




13 - Gurbacewar Ciki; Ga mai fama da, gurbacewa ciki , sai ya sa rabin cokali na man Habbatus- Sauda a cikin kofi daya kindirmo daya. Za ka sha sau biya a rana.




14 - Inganta Karfin Garkuwan jiki.

Shan man Habbatus-Sauda na karai nganta karfin garkuwar dan Adam musamman in zai juri shan rabin cokali a kowace rana.




15 - Ciwon Baya; Ga amasu fama matsalolin ciwon baya sai su , samu kamar cokali 1-2 na man Habbatus- Sauda sai ya dora akan wuta yayi dan dumi, wannan man zasu shafa a bayan su tare da yiwa wajen tausa , a hankali. Sannan su sha man Habbatus- Sauda, karamin cokali sau uku a rana.




16 - Rage Damuwa; Ga masu fama da yawan damuwa , ko kuma su ji duk sun takura , sai su sa rabin cokali na man Habbatus- Sauda a shayi ko kuma a kofe ( coffee).




17 - Matsalolin Al'adah; Mace mai fama da matsalolin da suka shafi al’ada sai ta samu zuma cokali daya ta zuba a kofin ruwan dumi, sannan ta sa karami cokali na man Habbatus-Sauda, sai ki sha sau biyu a rana, har na tsawon kwana 40.

Comments