Main menu

Pages

AMFANIN MAN KWAKWA GUDA SHA DAYA DA BA KOWA YA SANI BA

 



Amfanin Man Kwakwa Guda 11 Da Ba Kowa Ya Sani Ba:

Masana a fannin kiwon lafiya sun nuna cewa, za a iya amfani da man kwakwa wajen rage tumbi ko kiba ga mutanen da kiba ta yi mu su yawa. Baya ga haka, ana amfani da shi wajen magance Amosanin ka, hakanan ana amfani da man kwakwa a matsayin sinadarin wanke kai (Shampoo). Hakazalika ana amfani da shi don gyaran gashi da gyaran fata da sauran su kamar yadda bayani zai zo a kasa. Da fatan a sha karatu lafiya.




1. Gyaran Fata.

Ba shakka man kwakwa ya shahara wajen gyaran fatar jikinmu, kamar yadda mu ka fada a sama saboda sanin amfanin man kwakwa a fannin gyaran jiki ya sa kamfunan samar da mayukan gyaran gashi da na fata ke amfani da man kwakwa don sarrafa kayan da su ke samar wa jama'a. Saboda haka  za a iya amfani da shi don samun kyakkyawar fata mai sheki, haske da kuma laushi.



Ba tare da mutum ya hada man kwakwa da komai ba, zai iya shafa shi a jikinsa don maganin bushewar fata. Don haka ga ma su fama da matsalar bushewar fata sai mu ce, nesa ta zo kusa, sai su jarraba ku ma za su ga abin al'ajabi. 



Hakanan, shafa man kwakwa na maganin waskane, kyasbi da kuma tamojin fata. Baya ga wannan ko da mutum ba shi da daya daga cikin wadannan matsaloli da mu ka zana a sama zai iya amfani da man kwakwa saboda yana kara kyau da laushin fata.



Kuma idan ana maganar maganin nankarwa ne, anan sai mu ce man kwawa na sahun gaba a wannan fanni. Duk mai fama da matsalar narkanwa sai ta yi amfani da man kwakwa, kuma  shafawa kawai za ta yi a jikinta, sannu a hankali za ta ga nankarwa ta bace, fatarta ta yi sumul. Ko kuma idan mace tana gudun samun narkanwa bayan ta samu juna biyu sai ta samu man kwakwa ta ke shafa wa, to ba za ta fito mata ba.



Hakazalika, man kwakwa na maganin kurajen fuska, musamman ga maza dake yawan yin kurajen fuska, sakamakon gyaran fuska, idan su ka yi amfani da man kwakwa, in sha ALLAHU za su samu afuwar kurajen fuska.



Baya ga kurajen aski, hakanan, man kwakwa na magance kurajen fuska da aka fi sani da finfus. Duk wanda ke fama da wannna matsala sai ya juri shafa man kwakwa a fuskarsa, da iznin Allah zai rabu da finfus.




2. Gyaran gashi.

Man kwakwa wani sanadari ne da ya yi suna wajen maganin amosanin ka, kamar yadda mu ka rubuta tun da farko a sama, sannan ya na hana bushewa da karyewar gashi, sakamakon haka kuma sai ya samarwa da mace yalwataccen gashi mai sheki da tsayi. 




3. Maganin Fason Kafa.

Man kwakwa ya na maganin faso, ga mai fama da wannan matsala sai ya samu man kwakwa ya zuba gishiri ciki amma ba mai yawa ba ya gauraya su, ya ringa shafawa a kafar,  sannu kan hankali zai ga bushasshiyar fatar na barewa da kanta, sannan kafar za ta yi laushi, yadda za ta daina fashewa.




4.  Samar Da Kuzari Ga Jiki.

Ga mutanen da ke kukan nauyin jiki ko kasala sakamakon yawan maiko a jikinsu, sai mu ce, albishir gare su. Yin amfani da man kwakwa zai magance mu su wannan matsala cikin sauri. Kodayake, ana ganin man kwakwa a matsayin mai dake kunshe da maiko, sai dai masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, shi maikonsa ba mai lahani ga jiki ba ne, saboda haka ne ma  ya ke taimaka wa wajen narkewa da kuma fitar da duk wani maiko da ke da lahani ga jikin mutum, hakan sai ya haifarwa da mutum samun kuzari da walwala. 



Idan mutum na son amfanuwa da wannan fa'ida ta man kwakwa, sai ya ke zuba man kwakwar cikin abinci ko cikin lemon don samun karin kuzari da karfi ga jikinsa.




5. Inganta Garkuwar Jikin Dan-adam 

Man kwakwa na kara inganta garkuwa jikin dan adam sakamakon ya na kunshe da sanadarai irin su, lauric acid, capric acid da caprylic acid.  Bincike ya nuna wadannan sinadarai na matukar taimaka wa wajen bunkasa garkuwar jikinmu, hakan kuma na bayuwa ga kare jiki daga kamuwa daga kwayoyin cututtuka da ke haddasa wa mutum rashin lafiya.



6. Saurin Narkar Da  Abinci

Wani lokacin mutane kan yi fama da murdawar ciki sakamakon cushewar ciki wanda rashin narkewar abinci kan haddasa, bincike da masana a fannin kiwon lafiya su ka gudanar ya nuna yadda man kwakwa ke tasiri kan wannan matsala ta rashin narkewar abinci. Don haka duk mai fama da matsalar sai ya yi amfani da man kwakwa don samun waraka.





7.  Inganta Lafiyar Hakori 


Man kwakwa ya shahara wajen kara karfi da lafiyar hakori, sannan ya na kare wa mutum daga kamuwa da cututtukan da kan shafi hakori da kuma dasashi. Dalili kuwa shine man kwakwa na kunshe da wasu sanadarai na 'Calcium' da ke da tasiri wajen wannan aiki.




Baya ga karin karfi da kuma kariya ga hakora, hakazalika, man kwakwa na sanya hakora su yi haske da fari. Idan ana son samun wannan fa'ida, sai a hada man goge hakori da shi. Yadda mutum zai hada man kuwa shine, zai hada man Kwakwa da ‘Baking Soda’ ya gauraya su waje guda, ya samu 'brush' ya ke goge bakinsa da shi. Zai sha mamaki.



8. Saurin Gusar Da Kayan Kwalliya Daga Fuskar Mata.

Kowa ya san yadda mata kan yi amfani da kayan kwalliya a fuskarsu, kaamr hoda, jagira ko 'eye shadow'  da sauran su. Wani lokacin gusar da su ta hanyar gogewa ko wanke wa kan bata lokaci, kuma hakan bai cika sanya kwalliyar ta fita fes ba. Don saurin gusar da kwalliya kuma cikin sauki, ki shafa man Kwakwa kadan a jikin auduga ko kyalle mai tsafta ki goge fuska da shi, sannan sai ki wanke fuskarki.





9. Hana Fashewar Lebe.

Ga wadanda lebansu ke yawan fashewa sai su samu man kwakwa su ke shafawa a leban akai-akai, zai hana tsagewar leben ta hanyar hana shi bushewa. Idan mutum ya na kyamar yin amfani da man kwakwa zallarsa, sai ya kwaba shi da wani man ya ke shafa wa.






10. Maganin Kwarkwata.

Magani ne da aka gwada kuma aka ga fa'idarsa. Idan kina fama da kwarkwata ki ringa shafa man kwakwa a kanki tun daga matsirar gashinki har zuwa ilahirin gashin baki daya. Hakanan za ki iya hada man kwakwar da ruwan kal ki ringa shafawa a kanki. Hakika za ki ga aiki da cikawa.





11. Maganin Mura.

Bincike ya tabatar da cewa, man kwakwa na maganin mura da kuma ciwon makogoro. Idan mutum na fama da mura ko kuma ciwon makogoro sai ya ringa zuba cokali 2 zuwa 3 na man kwakwa cikin ruwan shayi ya na sha, ko kuma ya ke zuba man kwakwa da kuma man tafarnuwa cikin shayin ko ruwan zafi da ikon Allah zai samu sauki.


Comments