Kadan daga cikin amfanin Man Ridi ga Lafiyar jiki, wajen inganta k'ashi, Hakori da gyara gashi.
Amfanin man ridi ga kiwon lafiyar dan-adam na da yawan gaske sai dai mutum ya ambaci iya wadanda Allah Ya sanar da shi, sakamakon yadda har yanzu ake gudanar da bincike kan magungunan da za a iya samu daga man ridi.
Daga cikin amfanin man ridi ga lafiyarmu har da inganta lafiya da karawa gashi kyau, haka nan ana amfani da man ridi wajen gyaran fata, man ridi na taimakawa wajen kara karfin kashi, da kula da lafiyar zuciya, baya ga amfani da man ridin da ake wajen rage damuwa. Har ila yau, man ridi na taimakawa wajen inganta lafiyar jarirai da kuma ba su kariya daga wasu cututtuka da sauran su.
Saboda haka wannan shafi na ku mai farin jini na "Lafiyar Iyali" ya himmatu don kawo mu ku irin tarin baiwar da Allah Ya yiwa ridi, da kuma irin amfaninsa ga lafiyar dan-adam.
1. Gyaran Gashi
Al'ummomin daban-daban na amfani da man ridi wajen gyaran gashi tun shekaru aru-aru da su ka gabata. Baya ga haka, a wani bincike da aka gudanar kan amfanin man ridi ga lafiyar dan-adam ya nuna cewa, man ridin na kunshe da wasu sanadarai da ke taimakawa wajen hana zubewar gashi da kuma wanzuwar launin gashi.
2. Man Ridi Na Inganta Lafiyar Kashi
Binciken masana ya gano yadda ridi ke kunshe da sanadaran 'Copper da kuma calcium' wadanda ke taka muhimmiyar rawa wajen girma da karfin kashin dan-adam. Wannan na nufin cewa, matukar mutum ya rinqa zuba man ridi cikin abincinsa na yau da kullum, ba shakka ya kama hanyar samun lafiyayye kuma kakkarfan kashi. Har ila yau man ridi na taimakawa mutanen da shekarunsu su ka fara ja, su samu kwarin kashi.
3. Man Ridi Na Inganta Lafiyar Hakori
Man ridi na taimakawa mutane su samu kariya daga wasu cututtukan hakori da dasashi. Wannan dalili ya sa, likitocin hakori ke bai wa jama'a shawarar amfani da man ridi domin riga-kafin kamuwa da cututtukan hakori da kuma inganta lafiyar bakinsu gaba daya. Likitocin sun ce, mutum zai iya samun kariya daga ciwon hakori ko dasashi ta hanyar kurkurewa bakinsa da man ridi.
Comments
Post a Comment