Faidojin Tsamiya, Amfanin ta da Kuma Illolin da take dashi.
Tsamiya na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan da al’ummar Hausawa ke amfani da su sosai a rayuwar su ta yau da kullum. Ta na da amfani mai tarin yawa, haka kuma ta na wasu illoli idan aka sha ta ba bisa ka’ida ba.
Ana amfani da tsamiya wajen sarrafa abubuwan sha, wajen yin magani, da kuma a girke girke a matsayin abun dandano.
Wannan shafi ya gano matsalolin da Tsamiya ke magancewa kamar haka:
1. Cushewar ciki da rashin yin bahaya
2. Mura da zazzabi
3. Ciwon ciki
4. Tashin zuciya ga masu ciki
5. Tsutsar ciki
6. Matsolin da suka shafi hanta da madaciya
Illolin Tsamiya ga jikin Dan Adam
1. Tsamiya za ta iya haifar da illa ga masu ciwon sukari saboda ta na rage adadin sikarin da ke cikin jini. Haka ma ga wadanda za a yi wa tiyata, ana so su dakatar da shan tsamiya akalla makonni biyu kafin a yi tiyatar saboda wannan dalili.
2. Ga ramammu, yawan shan tsamiya na iya kara rama. Ga masu kiba kuwa za ta taimaka masu wajen rage kiba
3. Ba a son a shan tsamiya da magungunan Ibrofen da Aspirin saboda ta na kara adadin su da ke shiga jini. Idan haka ya faru, magungunan ka iya yin yawa su haifar da matsala.
Comments
Post a Comment