Main menu

Pages

BAYANIN AMFANIN HADA MALTINA DA PEAK WAJEN KARIN JINI

 


Bayani akan Maltina da Peak da wasu ke Shan don Karin jini, da abubuwan da suka kunsa.

Da yawa za kaga a kasar Hausa a lokacin da aka tabbatar da mutum yana da karancin jini, ko tana dauke da juna biyu ko ta Haihu ta zubar da jini dayawa sai kaji ance a bashi maltina da peak milk, a fahimtar mutanen mu zai kara jini. 




Gaskiyar magana babu alaka tsakanin karin jini da Maltina da Peak milk, saboda wake kwara daya yafi Maltina da Peak milk wajen samar da sinadaran kara jini a jikin dan Adam.




Idan kun duba jikin gwamgwanin peak milk za kuga babu sidaran karin jini a ciki  ( not rich in iron) Haka Maltina ma Babu sinadaran kara jini a ciki.



Tambaya anan shine ta Ina Maltina da Peak milk yazama maganin karin jini ?

Amsa: wannan kawai al'adace ta mutanen mu ba tare da sanin abun ba.




Maltina na dauke da sinadaran:

- Calories

- Carbohydrates

- Fat 

- Vitamin

- No Iron




Peak milk na dauke da sinadaran: 

- Fat

- Carbohydrates

- Protein

- Salt

- Vitamin A and D

- No Iron



Jikin dan Adam yana samar da jini da kansa, shi jini yana bukatar sinadaran iron daga abincin da muke amfani.


Daga karshe ina bada shawara garemu kudin da muke kashewa wajen Maltina da Peak milk domin kara mana jini, muyi amfani da su wajen siyen abinci masu dauke da iron kamar :


- Wake

- kifi

- Nama

- kwai 

- Kaza

- Fara

- zogole 

- Cashew

- cavage

- salat

- Spinach

- da sauran su.


ALLAH ya kara mana lafiya gabaki daya.

Comments