Main menu

Pages

BORIN JINI DA ABUBUWAN DA KE HADDASA SHI DA YANDA ZA A MAGANCE




Abubuwan dake janyo Borin jini, da yadda Ake magancesa.


Borin jini a hausance In dai wannan ne bayada nasaba da iskokai.

Duk kan Jikin wani 'dan adam yana dauke da kwayoyin da ke kare jiki daga ciwukkan da zasu iya yi masa barazana a rayuwarsa.




Su wadannan kwayoyin garkuwar jiki Sukan tsayu domin kariyar jiki daga wasu cutukka masu yaduwa, Su wadannan kwayoyin garkuwar jiki kamata ya yi a ce su zauna jiran shigowar kwayoyin cuta, idan sun shigo jiki su yake su. 



To haka kawai kuma, a wasu lokuta, sukan rikice su yaki jiki, kwayoyin na garkuwar jiki na cikin jini sune ke dimaucewa, su rikice, wato su yi bori, maimakon su yi aikin da ya kamace su, na yakar kwayoyin cuta ko yakar wani bakon abu da ya shigo cikin jini, sai su fara yakar bangarorin jiki. 



Yawanci abinda ke haddasa wannan shi ne shigar kwayoyin cutar jini, ko canjin abinci ko abin sha ko ganin wani abin kyama koma tunanin abin, da kuma canjin yanayi.




Wasu kuma akwai gado, wato sun gaji kwayoyi masu kawo wannan matsalar, wasu ko cizon kwari ko jin kanshin wani abu da jikinsu bayaso sukayi sai wannan matsalar ta tashi.




Irin wannan Matsalar fararen kwayoyin jini suke yin yawa sosai, na jajayen kwayoyin jini da platelets kuma su yi kasa sosai. 


Da yake kwayoyin garkuwar jikin mutum suna zaune cikin jikinsa dindindin, babu wani magani a likitance da aka sani mai warkar da wannan ciwo gaba daya, sai dai masu sa borin ya lafa, wato masu rarrashin kwayoyin su daina bori.




Akwai kuma wasu magunna masu rage karfin wadannan kwayoyin halittu masu yakar jiki. Sai dai kuma akwai wani abu da ake gudu zai iya faruwa bayan rage su, domin kwayoyin cuta zasu iya saurin shiga jikin mutum su kawo wani ciwon na daban.




Mai fama da wannan Matsalar zai iya saukarda wannan matsalar ta hanyar Hada Madara Cokaki 3 da zuma Cokali 2a sha In shaa Allahu za'a samu sauki da gaugawa.


Allah ya bamu lafiya.


Comments