Main menu

Pages

HANYOYI GUDA SHIDA DA ZAKU BI DON KAUCEWA CUTAR BASIR

 



Hanyoyi guda shida da zaku bi domin kaucewa Kamuwa da Cutar Basir

Basir wanda ake kira da "hemorrhoids" ko kuma "piles" a turance, larura ce da ke ci gaba da shan gurguwar fahimta a tsakanin al'umma.




A likitance, ba wani abu ne basir ba face kumburarrun jijiyoyin jini a cikin ƙarshen babban hanji da kuma dubura. Waɗannan kumburarrun jijiyoyin jini su ne suke talewa har su yi bulli cikin ƙarshen babban hanji ko kewayen dubura. Basir a cikin ƙarshen babban hanji shi ne "basir cikin dubura" yayin da basir a kewayen dubura shi ne "basir wajen dubura". 




Haka nan, "basir mai tsiro"  ci gaban "basir cikin dubura" ne wanda ke bayyana yayin da  matsalar ta je matakin ƙarshe. "Basir mai tsiro" na faruwa ne sakamakon zazzagowa ko saukowar jijiyoyin jinin da suka yi bulli zuwa wajen dubura, musamman yayin yunƙuri.




Alamomin "basir cikin dubura"

Bayyanar alamomin basir ya danganta ga wane irin basir ne ya bayyana, "basir cikin dubura" ko kuma "basir wajen dubura".


1. Zubar jini ba tare da jin ciwo ba yayin tsuguno.


2. "Basir mai tsiro" wanda ke fitowa wajen dubura har sai an tura da yatsa domin mayar da shi. Yana haifar da ciwo da raɗaɗi.



Alamomin "basir wajen dubura":

1. Ciwo mai raɗaɗi


2. Ƙaiƙayi 


3. Kumburi a kewayen dubura


4. Zubar jini yayin yunƙurin tsuguno.


Sabuban da ke kawo basir


Basir na faruwa sakamakon takura jijiyoyin jini a dubura har su kumbura sannan su yi bulli saboda abubuwa kamar haka:


1. Yawan yunƙuri yayin tsuguno.


2. Tsawaitar lokacin tsuguno.


3. Fama da atini ko kuma taurin bayan gida tsawon lokaci.


4. Kasancewa mai Ƙiɓa / teɓa.


5. Kasancewa mai juna biyu.


6. Cin abincin mai ƙarancin dusa, harza ko ganyayyaki.


7. Ɗaga nauyi akai-akai da sauransu.


Hanyoyin Kiyaye Basir Cikin Sauƙi


Hanya mafi kyau wajen kiyaye kai daga basir ita ce sanya bayan gida ya zamo mai taushi yadda zai fice ba tare da yunƙuri sosai ba.


Waɗannan hanyoyi za su taimaka wajen kiyaye kai daga basir da kuma rage matsalolinsa:


1. Cin abinci mai dusa sosai: Abinci mai dusa sun haɗa da 'ya'yan itatuwa, ganyayyaki da kuma datsar hatsi.


2. Shan isashshen abinsha: Shan isashshen ruwa aƙalla lita 2 — 3 kowace rana da sauran ababen sha masu ruwa-ruwa.


3. Rage yunƙuri yayin tsuguno: Yunƙuri tare da riƙe numfashi yayin tsuguno na takura jijiyoyin jini a cikin dubura.


4. Garzayawa da zarar jin bayan gida: Yin buris da bayan gida yayin da aka ji shi na janyo jiki ya ci gaba da tsotse ruwan bayan gidan har ya yi tauri.


5. Atisaye: Atisaye ko motsa jiki na taimakawa rage taurin bayan gida. Haka nan, atisaye na taimakawa wajen rage ƙiba wanda hakan zai rage nauyi ko takura ga jijiyoyin jini a cikin dubura.


6. Kauce wa dogon zama: Dogon zama musamman yayin tsuguno na ƙara takura jijiyoyin jini a dubura.


Basir larura ce da ake warkewa sumul bayan amfani da magunguna da sauran hanyoyi a likitance. Amma idan basir ya yi tsanani yin tiyata na iya zama tilas.


Tuntuɓi likita da zarar alamun basir sun bayyana maimakon shan magungunan gargajiya da ba ka da tabbacin ingancinsu.

Comments