Kotun Koli ta Najeriya ta dakatar da wa'adin daina karbar tsofaffin kudade a 10 ga wannan watan.
Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da gwamnatin tarayya daga aiwatar da wa'adin amfani da tsofaffin takardun kuɗin kasar.
A baya dai CBN ya saka 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsofaffin takardun naira 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sauya wa fasali.
Jihohin arewacin ƙasar uku, waɗanda suka haɗa da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da ƙarar a gaban Kotun Ƙolin ƙasar suna buƙatar kotun da ta hana Babban Bankin ƙasar aiwatar da wa'adin.
A hukuncin wucin-gadin da suka yanke, alƙalan kotun bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari'a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin tarayya da Babban bankin ƙasar da sauran bankunan kasuwanci na ƙasar daga aiwatar da wa'adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.
Kotun ta kuma ce dole ne gwamnatin tarayya da CBN da kuma sauran bankunan ƙasar su jingine batun aiwatar da wa'adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin a ranar 15 ga watan Fabrairu.
Wannan hukunci na nufin a halin yanzu al'ummar Najeriya za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin ƙasar har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukuncin ƙarshe.
Batun wa'adin amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar dai ya zama wani batu da ya ɗauki hankula a 'yan kwanakin nan.
Rabuwar kawuna game da wa'adin
Hankulan 'yan ƙasar sun rabu game da wa'adin, inda wasu ke ganin ya kamata a tsawaita wa'adin, a gefe guda kuma wasu na ganin bai dace a tsawaita ba.
Daga cikin waɗanda ke ganin ya kamata a ƙara wa'adin har da ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki, wadda ta gana da shugaban ƙasar a makon da ya gabata kan lamarin.
Bayan ganawar ƙungiyar ne kuma jihohin Kaduna da Kogi da Zamfara suka shigar da ƙara gaban Kotun Ƙolin ƙasar suna masu buƙatar kotun ta dakatar da CBN ɗin daga aiwatar da wa'adin.
Saboda a cewarsu mutane fuskantar matsalar ƙarancin sabbin kuɗin da suka ce ya jefa al'umominsu cikin mawuyacin hali.
Jihohin uku sun ce tun bayan bayyana fara amfani da sabbin takardun kuɗin, ake samun matsalar ƙarancin sabbin kuɗin a jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara.
Sun kuma ce mutanen da suka kai tsofaffin takardun kuɗin nasu bankuna, na shan matuƙar wahala kafin samun kuɗaɗen daga bankunan, a wasu lokutan ma ba su samun kuɗin domin gudanar da rayuwarsu ta yau-da-kullum.
To sai dai a gefe guda gamayyar jam'iyyun siyasa 13 a ƙasar sun yi barazanar ƙaurace wa babban zaɓen ƙasar da ke tafe matukar Babban Bankin Ƙasar ya ƙara wa'adin amfani da tsoffin kuɗi a ƙasar.
Gamayyar ƙungiyar shugabannin jam'iyyun, waɗanda suka yaba wa shugaban ƙasar Muhammadu Buhari kan sauya fasalin takardun kuɗin ƙasar, sun dage cewa dole a tabbatar da tsarin.
Comments
Post a Comment