Main menu

Pages

KUSKUREN DA WASU IYAYE KE TABKAWA LOKACIN AUREN DA 'YA'YAN SU

 



Manyan Matsalolin da ake tafkawa a duk lokacin da za a Aurar da Mace.

Abinda na fahimta a aure a yau shine da yawan mutane suna dauka jima'i shine rayuwar aure ba mazan ba ba matan ba kai harma da iyayen mu mata....




Abinda zai baka mamaki shine daga lokacin da akace yau ansaka ma yarinya ranar aure, madadin ace iyayen mu su koya mata yadda rayuwar auren ke tafiya  da sauransu da yadda zata kula da mijinta bisa hakuri da miji..




A'ah da yawa iyayen mu bawai wannan bane a gabansu. Daga lokacin ne zasu bazama nema ma yarinya magunguna na mata. 


Domin burinsu shine namiji yaji dadinta a rayuwar aurenta. Ita koh yarinya ce karama bata san meye rayuwar aure bah shi kanshi first, ammah kuma idonta zai bude da  jima'in auren. zataji gaba daya ta tsorata ma da auren.




Idan namijine wadda bai taba kusantar wata mace a rayuwarshi bah (mara aure) a lokacin farko zaiji gaba daya auren ma yafita a rayuwarshi kunsan meye babban daliin to shine wannan hadin da iyaye sukama yariyan yafi karfin kanshi da tunaninshi..





Ita kuma mace a lokacin babu abinda zata so a rayuwar aurenta sama da wanna jima'in domin gaba daya shi idonta yafi budewa akai, wanda taga iyayen sunfi maida hankali a kanshi..




Da yawa zakaga maza da matan mu a yau sunfi daukar jima'i sama da komae a rayuwar aure namiji bai iya tarairayar matarshi bah itama matan batasan ya zata kula da mijin ta bah.. karshe kulawa da juna ya gagara..




𝐍𝐎𝐓𝐄::-  Yadda iyayen mu suka maida hankali ga tsuma yarinya inzatayi aure da koya mata rayuwar aure sukayi.. ina mai tabbatar ma da da yawan aure bai samu tangarda bah domin shi aure ba jima'i bane kawae nadan lokaci a'ah xaman takewa neh akeso na har abada da kaunar juna bisa kyautata ma juna


Comments