Kurakuren da Mata suke tafkawa lokacin daukewar jinin Al'adah, da ya kamata kowace Mace ta gyara
Mafi yawan mata idan jinin al'ada ya 'Dauke musu suna jinkirta wanka da niyar ko jinin zai Qara dawowa.
Wasu sukan Qara kwana 'Daya zuwa biyu bayan haila ya 'Dauke.
Wasu kuma idan suka ga alama guda 'Daya na 'Daukewar jinin, sai suce zasu jinkirta wanka domin su jira zuwan sauran alamomin. Misali: Mace taga bushewar gaba amma bata ga Farin ruwa ba, wanda ake kiransa da larabci ( ﻗﺼﺔ ﺍﻟﺒﻴﻀﺎﺀ ), daga nan sai tace bari ta bari sai farin ruwa yazo sannan tayi wanka ta cigaba da sallah da azumi.
Duka Wannan kuskure ne babba
Abinda yake wajibi shine: Da zarar taga jini ya tsaya ko taga alamomin Daukewar Jinin haila, toh wajibi ne tayi wanka nan take ta cigaba da ibadar ta. Qin yin wanka har lokacin sallah ya wuce babban zunubi ne.
Allah Ya tanadi Azaba mai tsanani ga masu wasa da sallah.
Allah yace:-
" ﻓَﻮَﻳْﻞٌ ﻟِﻠْﻤُﺼَﻠِّﻴﻦَ ( 4 ) ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻫُﻢْ ﻋَﻦْ ﺻَﻠَﺎﺗِﻬِﻢْ ﺳَﺎﻫُﻮﻥَ "
} ﺍﻟﻤﺎﻋﻮﻥ : 4-5 }
Allah ya qara da cewa:-
" ﻓَﺨَﻠَﻒَ ﻣِﻦْ ﺑَﻌْﺪِﻫِﻢْ ﺧَﻠْﻒٌ ﺃَﺿَﺎﻋُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻭَﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﺍ ﺍﻟﺸَّﻬَﻮَﺍﺕِ ﻓَﺴَﻮْﻑَ ﻳَﻠْﻘَﻮْﻥَ ﻏَﻴًّﺎ "
} ﻣﺮﻳﻢ : 59 }
...... Da ayoyi masu yawa cikin al-Qur'ani.
daga lokacin da jini ya 'Dauke, ibada ya wajaba ga mace.
Idan mace ta jinkirta sallah toh sai ta rama su bayan tayi wanka, sannan tayi istigfarin jinkirin sallah
Idan kin karanta kiyi Qoqarin turawa yar uwarki musulma zaki samu lada in shaa Allaah.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
Allah yasa mudace
Comments
Post a Comment