Siffofin kyakkyawar Mace Guda biyar da ya kamata kowa yasani, don yasan wacece Mace kyakkyawa.
Macen da tafi kowacce kyau ba fara bace ba ja ko baƙa ba, ba doguwa bace ko gajera, ba me manya ko ƙananun idanu bace, kuma hakanan ba me tsayin gashi ba ce ko mara gashi, kuma ba me sanya kaya na alfarma ko akasin haka bace.
Kyakkyawar Mace
- Itace wacce take tsoron Ubangijin ta tare da fifita dokokin Sa akan son ranta tare da ɗaga darajar ahalinta da tarbiyyan da suka bata da kuma kyawawan dabi'unta ba wai da adon ta ko kyawun ta ba.
Kyawun Mace yana ga tarbiyan ta da kuma Kunyar ta.
Kyakkyawar Mace
- Itace mai kame kanta tare da girmama duk wani namijin da Allah ya ɗora masa ragamar ta.
Kyakkyawar Mace
- Itace wacce bata barin wani yayi wasa da ita ko tunanin ta kuma ta ke ɓoye adon ta da hijabinta.
Kyakkyawar Mace
- Itace wacce take taimakawa wurin tseratar da 'yan uwanta maza daga fitina ta hanyar ƙanƙan da kanta, Kunyar ta, da kuma kamewar ta.
Kyakkyawar Mace
- Itace wacce ta ɗauki kanta tamkar sarauniya saboda ƙimar da Allah yayi mata, bata bayyana adon ta, tabarruj, sanya turare ko kwalliya ga wanda ba muharramin ta ba don a kira ta da kyakkyawa domin ta yarda cewa:
الجمال في التربية وحسن الخلق والقلب النقي الصالح والتفقه في الدين.
Wannan itace Macen da tafi kowacce kyau da ƙima, lu'u'lu'u mai tsada, kuma ita ɗin taskace..
المرأة الصالحة هي أفضل من كنوز الدنيا
اللهم ارزقنا تاج التقوى والصلاح وارشدنا لسبيل الهدايه والفلاح
أمين يارب العالمين
Comments
Post a Comment