Sirrukun dake cikin Zuma da Kuma Amfaninta ga Al'ummah wajen nagani.
Haƙiƙa ita zuma tana daga cikin manya - manyan abubuwan da ake magani da su kuma itama kanta magani ce domin ya zo a cikin alkur'ani mai girma
Inda Allah (S.W.T) yake cewa:
wato yana futowa daga cikinta (ita zuma) wani abun sha wanda yake mai launuka daban-daban hakika a cikinsa akwai waraka ga mutane
Zuma akwai
Fara
Baka
da sauran kaloli kuma tana da magani ko wacce daga cikin ta
haka nan yazo a cikin hadisin Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:-
Na hore Ku da ababan waraka guda biyu (2) zuma da alkur'an (ibn majah da Hakim suka ruwaito wannan hadisi).
- Bayan haka an ruwaito cewa: wani mutum ya zo wajan Manzon Allah (S.A.W) yace : yaa Manzon Allah na zo ne in gaya maka cewa dan uwana yana fama da ciwon ciki, sai Manzon Allah ya ce jeka ka shayar da shi zuma, sai ya Tafi ya shayar da shi zuma amma bai warke ba, sai ya koma wajan Manzon Allah ya sake cewa jeka ka shayar da shi zuma, sai yaje ya shayar da shi, amma bai warke ba, sai ya komo wajen Manzon Allah sai Manzon Allah yace da shi hakika Allah yayi gaskiya, cikin dan uwanka yayi karya, jeka ka sake shayardashi zuma, da yaje ya sake shayar dashi zuma sai ya warke
wannan hadisi yazo cikin (bukhari da Muslim)
Haka nan wannan yana daga cikin abun da ya kamata mu fa'idantu da shi cewa shi magani ba'a yi masa gaggawa, Ana so adinga mai-maitawa da haka har Ubangiji Ya kawo saukin cutar.
Haka nan yana daga cikin sirrin zuma zaka ga yawancin magani ana cewa hada shi da zuma farar saka.
- Yana daga sirrin zuma in an haifi yaro ya Kai kamar wata hudu (4) kullum a dinga diga masa a baki sau uku (3) a Rana saboda ta Kara masa wayo da basira da kaifi hadda in ya girma. sannan tana sa qashinsa ya Kara kwari.
- Yana daga sirrin zuma mace mai jego ta dinga shan zuma a kullum itama sau uku (3) a Rana kafin ta haihu da bayan ta haihu saboda samun cikakkiyar lafiya da ita da yaronta.
Comments
Post a Comment