Main menu

Pages

WASU ABUBUWA DA MA'AURATA ZASU KIYAYE DON WANZUWAR FARIN CIKINSU

 



Abubuwan Da Za A Kiyaye Domin Samun Farin Cikin Zaman Aure:


Kowa yana son farin ciki, amma ‘yan kadan ne suka fahimci yadda za su samu farin cikin daga wajen iyali. Wanda ya ke zaton yin aure da kyakkyawar mata, katon gida ko samun babban mukami shi ne hanyar farin ciki, to yana yaudarar kansa ne kawai. Akwai wadanda suke aurin mata kamar larabawa, daga baya sai su auri mummuna.



Soyayyar da ke tsakanin mace da namiji abar sha’awa ce kawai ga wanda ba da shi ake ba. 

Don haka muka fi son ganin fim din Indiya fiye da yadda muke son zaman gida da iyali.




 Mafi yawan abin da ke cikin aure kuwa hakuri ne dai da ake gaya mana. Duk kuwa abin da ake cewa hakuri ne, to a cikinsa kai ka san wahala ce a kewaye da shi.



 A cikin soyayya tun asali ba komai sai bakin cikin kishi da son kai yake janyowa. Wanda ya kira budurwarsa ya ji tana waya, zai gaya maka bakin cikin da yake ciki ya ninka duk wani farin ciki da yake samu a lokacin da suke yin wayar awanni. Kullum cikin fargabar kada a kwace maka budurwa kake, karshe kuma bayan auren, mafi yawan ma’aurata suna da-na-sanin auran wanda suka aura.




Wanda yake zaton katon gida ko wani mai cike da kayan alatu shi ne farin ciki, to bai san mene ne farin ciki ba. Masu tallace-tallace a kamfanoni suna yaudararmu da nuna mana katon gida hade da iyali suna dariya domin mu siyo kayansu. 




Amma kuma ba sa gaya mana cewa sati daya na farko kana gidan ya isa ka dena ganin kyansa.


Ba mu fahimci mene ne farin ciki ba, don haka ba za mu iya samun sa ta hanyoyin da muke zato ba. 




Wanda yake dauka farin ciki wani mataki ne da ake zuwa don a same shi, to ya yaudari kansa da kansa. Wanda ya dauka farin ciki samun wasu abubuwa ne, to ya yaudari kansa da kansa. A haka kuma mutane suke ci gaba da yaudarar kansu da kansu ba su sani ba.




Idan kama so ka samu farin ciki daga wajen iyalinka, to dole sai ka bai wa iyalanka hakkinsu wanda yake kan wuyanka. Yana da kyau mai gida ya san duk wani hakkin da ya rataya a wuyansa na aure, ta sannan hakkin ka ne za ka iya kyautata wa iyalinka domin kai ma ka samu farin ciki a cikin gidanka. 




Ma’aurata da dama sun rasa farinciki ne a cikin gidajen su sakamakon rashin saukar da nauyin da ya rataya a kansu. Har yanzu wasu ma'urata ba su san nauyin da ya rataye a wuyansu ba na aure, to ta yaya mutum zai samu farinciki a cikin gidansa. 




Dole sai mun san hakkin zama da iyalanmu kafin mu iya kyautata musa, sannan suma su samu farinciki a cikin gidajanmu. Ya kamata ma’urata su kula da yadda suke yin kuskure wajen zama da iyalai, sannan su dauki matakin gyara a matsayinka na jagoran gidanka.


Allah Ya sa a mu dace da dukkan Alkhairi, Ya wanzar da zaman Lafiya da farin ciki a kowane gidan aure. Ameen 

Comments