Hanyoyin da zakiyi Amfani da Tuffa (Apple) Wajen gyaran fatar jiki da Fuska.
Shan Tuffa daya a rana na kawar da cututtuka da dama, kuma yawan shansa na rage tsufa da wuri. Idan ana son maganin rage tsufa, ba sai an kashe kudi masu yawa a kansu ba. Sai a rika sayen Tuffa ana sha. Yin hakan na rage bayyanar tsufa a jiki da fuska. Tuffa na dauke da sinadaran bitamin C da A. A yau na kawo muku yadda za a yi amfani da Tuffa a fuska domin rage tsufar fuska da jiki.
1- Tuffa da zuma: A markada ko a jajjaga Tuffa sannan a zuba zuma cokali biyu a kwaba da kyau. Sai a wanke fuska da sabulu kafin a shafa kwabin da aka yi. Sai a wanke bayan minti talatin. Yawan amfani da wannan hadin, na sanya hasken fata.
1 - Ayaba da Tuffa: Ayaba na dauke da sinadarin gyaran fata da kuma na bitamin A da B da kuma C. Yin amfani da ita a fata mai gautsi na gyara fata. A kwaba ayaba bayan an bare ta sai a hada ta da markadadden Tuffa a kwaba da dama kafin a shafa a fuska. Za a iya zuba zuma ko kindirmo kadan a wannan hadi. A shafa a fuska na tsawon minti talatin kafin a wanke.
3 - Lemun tsami da Tuffa da kindirmo: Wannan hadi na sanya sulbin fuska. A markada Tuffa sannan a matsa ruwan lemun tsami da kindirmo, sai a kwaba. A shafa a fuska da wuya. Sai a wanke bayan minti ashirin.Wannan hadin na sanya laushi da sulbin fata da kuma dada wa fata haske.
Comments
Post a Comment