Main menu

Pages

YANDA AKE HADA FARAR HUMRA DON AMFANIN GIDA KO SANA'A




Yanda Ake Hada Farar Humra, don sana'a ko amfanin gida.

Zanyi bayanin yanda ake hada Farar Humra. Idan Allah yaso ya yarda.

Kayan da ake bukata wajen hada Farar Humra sune kamar haka;


1. Scenario (ruwan turare ne a roba)

2. Powder (hoda ce fara)

3. Musk (a roba yake yar karama)

4. Fantasia madarar turare

5. Passion madarar turare

6. Mukhallat badar madarar turare Yanda ake hada wa shine.




1. Xaki xuba Musk a cikin Scenario ki girgiza sosai

2. Saiki zuba powder itama ki girgiza sosai

3. Saiki dauko madarar turarenki suma ki

zuba ki girgiza.



Note! Idan kina hada wa ya kasance kisamu wani abu wanda zai dauke kayan gaba daya misali roban swan water zata yi.


Wannan hadin ana yinsa 1100 idan kuma aka cire mukhallat badar to 1000 ne gaba daya.

Ya danganta da irin kamshin da kike so ba dole sai wadan nan ba. Kuma tana riba ba laifi.

Comments