Yanda Ake Hada Sabulun Dettol da Dilka, ki koya don sana'a ko amfani dashi a cikin gida.
Yau zamu hada sabulun DETTOL da DILKA na maganin kuraje dasa kyan jiki. Kayan da za a bukata sune.
- Soda ash
- Caustic soda
- Palm kanel oil (p k o)
- Pince oil
- Clorofazinol
- Dilka
- Silicate starch
- SLS
Yadda zaa hada shine;
Za a debo ruwa kimanin liter 1 da rabi. Clean ruwa mai kyau da tsafta, sai a dauko caustic soda rabin gwangwani na madara sai a jikasa da ruwa Rabin liter 1/2 liter. Sai a motsa sosai a tabbatar ya narke sai a rufe a barshi yayi 24hr kwana 1.
Sai a dauko soda ash ita gwangwani 1. Sai SLS dan kadan kamar 1/8 na gwangwani sai a jikasu da ruwa kimanin Rabin liter 1/2 liter. Shi kuma koda 5hrs yayi ba matsala amma a tabbata an motsa sosai a lokacin da aka zuba.
Washe gari bayan sun hade a bude a tabbatar duk sun narke babu Wanda yayi kamar kankara ice so saiki samu wani waje ki tace shi saboda datti kowanne ki ware masa robansa.
Saura Rabin liter na ruwa saiki jika dilka ki motsa sosai.
Saiki dauko babban roba ki juye palm kanel oil liter 1 a ciki saiki dauko silicate starch ki motsa a ciki ki tabbatar ya motsu.
Saiki dauko taceccen ruwan caustic soda ki juye ki motsa idan ya hade saiki dauko na soda ash shima ki motsa ya hade.
Saiki dauko sauran ruwanki Wanda kika jika dilka ki tace shi shima saiki juyeshi a ciki ki motsa.
Sannan saiki dauko pince oil da clorofazinol ki juye ki motsa shikenan saiki juye a robobinki ki bashi Dan lokaci saiki rufe shikenan kin kammala sai a kai kasuwa
Abnda zaa kula dashi shine wajen zuba SLS a tabbatar an rufe baki da face mask, sannan kada a bari caustic soda ya taba jiki.
Haka zalika a tabbata cewa wajen motsawa ba ayin hagu a dawo dama, ma ana clockwise ko anti clockwise. So ake idan kanayin clockwise toh kada ka chanja kaitayi harki gama.
Wannan sabulun yana da riba ba laifi so ina son a jarabashi insha Allah ba za ai dana sani ba.
Comments
Post a Comment