Yadda zakiyi Amfani da Zobo wajen dai dai ta rikicewar Al'adah, da daukewarta gaba daya.
Zobo wanda mukasani da ake sarrafawa da kayan kamshi da irinsu citta da kaninfari asha domin samun nishadi to ba anan kadai ya tsaya ba zobo yana taka muhimmiyar rawa wajen inganta lafiyar dan adam misali.
Amfani da zobo yadda yadace babu shakka yana saukaka rikicewar Al'adah sannan yana maganin daukewar Al'adah da kuma inganta zuwan jinin Al'adar yadda ya kamata.
Idan kina fama da rikicewar Al'adah amfani da zobo yana taimakawa wajen daidaita Al'adar bugu da kari bayan magance rikicewar Al'adar to amfani da zobo yana maganin ciwon mara lokacin Al'adar.
Yana da kyau mata su fahimci kowace mace akwai yanayin yadda Al'adah ke zo mata, wasu Al'adah kan zo kowane wata wasu kuma sukan tsallake watanni kai wasuma tana zuwa farkon wata wani lokacin tsakiyar wata wani lokacin ma karshen wata, shi jinin Al'adah zai iya canzawa a kowane lokaci da wasu al'amurran rayuwa suka canza.
Mata da yawa sukan fuskanci matsalar rikicewar Al'adah lokacin da tsufa ke riskarsu ma'ana idan suna kusa da gama jinin Al'adar baki daya.
Hanyar da za kibi domin gane kina da rikicewar Al'adah ko akasin haka shine ki rubuta lokacin da jinin ke zo maki kowane wata sannan ki kirga kwanakin ki gani shin suna zuwa dai dai ko suna sabawa?.
Idan kika tabbatar da suna sabawa abinda zakiyi shine ki samu zobonki mai kyau kidafa kisa citta da kaninfari ki kirga daga ranar da kika fara period zuwa kwana sha hudu kisha duk bayan kwana daya har ranar da za ki fara wani period din saiki daina to insha Allahu duk wani matsalar period kowane iri zakiga chanji.
Allah yabamu dacewa Ameen.
Comments
Post a Comment