Yana Da Matukar Mahimmanci Ma’aurata Su San Wadannan Abubuwa:
Ya zama wajibi mu yi kokarin ganin wasu abubuwa na zamantakewa domin kaucewa matsaloli wanda rashin sani ke haifarwa.
Yana da matukar mahimmanci ma’aurata su san wadansu abubuwa a cikin zaman aure.
Domin dole ne a samu matsaloli a cikinsa, amma idan aka bi wasu hanyoyi sai matsaloli su zo da sauki ta yadda ba za su lalata zamantakewar ma’aurata ba.
Zaman aure wani abu ne da ake fatan daga lokacin da aka fara tunaninsa ya zamo wani abu na mutu ka raba, domin hakan ne zai tabbatar da cewa an san abin da ake nufi da aure da kuma irin halin da za a shiga. Sanin hakkin da ke kanka a matsayin miji, sanin matsayinki na mata a gidan aure yana da mahimmancin gaske, domin hakan ne zai ba da damar tabbatar da wanzuwar wannan aure.
Yana da kyau ma’aurata su sani, aure ba tsari ne na zama zuwa wani dan lokaci kayyadadde ba, wato da an cinye kayan gara an gama zakin amarci a kama masifa a rabu ba, a’a tsari ne da Allah ya shirya mana shi, sannan ya tsara mana yadda zamantakewar za ta kasance.
Allah Ya dora ma kowannensu, miji da mata wadansu dokoki. Idan muka ji tsoron Allah a cikin zaman auratayyarmu za mu kasance cikin wadancan biyun da na ambata a baya. Ya kasance zaman aure ne wanda a kowane hali kuka sami kanku za ku iya jurewa cikin yanayin jin dadi ko akasin hakan, cikin halin lafiya ko rashinta.
Idan har za ku iya jure wa wahalhalun da kuka yi ta sha lokacin da kuke samartaka me zai hana ku karfafi aurenku ya zama na har abada ba?
Yana da kyau ma’aurata su san halayyar junansu ta hanyar da babu yaudara, karya, ko cuwa-cuwa.
Ya kasance ma’aurata sun fahimci hanyar da za su iya sulhunta kansu ba tare da wani mutum na uku ya shigo tsakaninsu ba, hakan na samuwa ne ta irin yadda kowannensu ya fahimci matsayinsa a zamansu na ma’aurata.
Miji ya sani cewa ragamar tafiyar da gida a kansa yake. Idan aka fahimci wadannan shawarwari, to in Allah ya yarda za a samu kyakkyawan zamantakewar aure ta yadda ma’aurata za su zauna cikin farin ciki tare da kaucewa faruwar matsaloli masu yawa.
Ya ku ma’aurata, sanin wadannan abubuwa suna da matukar mahimmanci a gare ku ta yadda ba za ku sha wata wahalar zamantakewar aure ba.
Comments
Post a Comment