Yadda Ake Hadin Gumban Mata Don Samun Ni'ima.
Zaki nemi kayan hadi kamar haka;
- Gyada
- Kwakwa
- Ridi
- Dabino
- Mazarkwaila
- Nono/ Kindirmo.
Yanda zaki hada Wannan Gumba shine;
Zaki samu gyadanki sai ki soya da ridi sama sama sai ki dauko sauran kayan hadin sai ki hadasu guri daya sai ki dakasu dukka a turmi, haka zaki ta dakawa har lokacin da yayi laushi kuma ya koma ya dunkule.
Sai ki samu wuri mai kyau ki zuba ki dunga yanka kina damawa da nono kina sha, hmmmmm yar uwa idai kika juri shan wannan ai sai dai ki ba wata labari.
Comments
Post a Comment