Main menu

Pages

HANYAR DA MATARA DA TA HAIHU ZATA BI DON DAWO DA NI'IMAR TA

 



INGANTACCEN HADIN DA MATAR DA TA HAIHU ZATA YI DON DAWO DA NI'IMAR TA.

Akan samu wasu mata bayan sun haihu  suna fama da matsalar bushewa, suyi ta fama amma ni'imar taqi dawowa to ga waraka ta samu da izinin Allah..



Zaki nemi wadannan abubuwan 

1️⃣--Kankana

2️⃣--Kanimfari

3️⃣---Madara peak/Luna

4️⃣---Citta



Da farko Zaki samu kankana madaidaiciya ki fere ta kamar yadda ake feraye kabewa sai ki yanyankanta gaba daya da farin bayan da kwallon duka ki zuba a blender. 



Sanan ki samu kanimfari kamar cokali 1 ki dakashi ya zama gari, sannan ki daka citta itama cokali 1 sai ki zuba acikin blender ki markada ya niqu sosai sanna ki kawo madararki gwangwani daya ki juye ki sake markadawa. 



Sai ki samu mazubi ki juye, sai kisa firinji ta sanyi sanyi , Zaki Wuni kinasha har ya qare yar uwa zakiga abin mamaki, ki ga yadda zaki dunga zuba kamar korama.


   Haka Kuma ko wacce mace ma da ba haihuwa tayiba zata iya hadawa tasha.


Comments