Amfanin Garin Sassaken Marke wajen Maganin cututtuka daban badan.
Ko shakka babu, jikin mutum yana samun ginuwa ne da samun kariya daga matsaloli ta dalilin amfani da tsirrai, ko bishiyoyi da kayan maramari.
Hakika wannan bishiya ta marke, dukkan jikinta yana da amfani. Gasu kamar haka;
1. Saiwar bishiyar Marke:
Ana dafa ta da jar kanwa ana yi wa mai mutuwar barin jiki gashi da ruwan maganin mai dumi, sau biyu a rana, tare da shan ruwan maganin rabin kofi sau biyu a rana tsawon kwana Sha hudu za a samu lafiya da yardar Allah.
2. Sassaken Marke:
Idan aka hada shi da Jan kajiji aka nika suka zama gari sai a dinga shan cikin karamin cokali da ruwan dumi ko shayi, sau biyu a rana tsawan kwana bakwai. Yana maganin tari, asthma, kurajan huhu, taruwar ruwa a cikin huhu, daskarewar majinar kirji, numfashi da wahala, sanyin jiki da Kuma rashin karfin jiki.
3. Garin Sassaken Marke da sassaken tsamiya a zuba cikin Nono a na sha, Yana maganin Zazzabi, kasala, Ciwan jiki, Ciwan ciki, Amai, Gudawa, da kuma sassauta ciwon daji.
Allah yasa adace.
A turawa yan uwa su amfana
Comments
Post a Comment