Hanyoyin daban daban da zakiyi amfani da Madara don gyaran Jiki.
Madara na dauke da sinadaren da ke saurin gyara fata. Yawan bai wa yara madara na dada kaifin basira ga yaro. Bayan haka, shan madara na sanya fata sulbi da laushe da kuma kare fata daga gautsi.
•1)- A sami madara sannan a kwaba ayaba. A zuba ruwan madarar da ayabar ta dan yi kauri kadan sannan a rika shafawa a fuska na tsawon minti goma sha biyar a rana sannan a wanke. Yin hakan na sanya sulbin fuska musammanga mata
•2)- A sami madaran gari sannan a kwaba shi da ruwa sannan a matse ruwan lemun tsami a ciki sannan a gauraya a rika shafawa a fuska kafin a shiga wanka a kullum domin samun hasken fata.
•3)- Madara na goge dukanin daudar fuskar; za a iya samun rabin kofin madara sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke. Bayan hakan, sai a shafa a fuska da wuya a jira na tsawon minti 2 zuwa 3 kafin a wanke da ruwan dumi.
•4)- Madara na sanya fata sulbi domin hakane ya kamata a rika amfani da shi a matsayin cleanser ; a samo auduga sannan sai a tsoma a cikin madarar ruwa. Sai a rika goge fuskar da ita, sannan sai a jira ta bushe kafin a wanke, yin hakan na rage maikon fuska kuma da sanya fuska taushi da sulbi sosai
•5)- Za a iya amfani da madara a gashi domin kara wa gashi lafiya. Musamman lokacin sanyi, gashi yakan tsinke. Sai a zuba madara a gashi ya taba tsagun kai, sai a jira na dan minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi zubewa da tsinkewa.
•6)- Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin hakan na hana fashewar fuska lokacin sanyi
Allah Ya bada sa'a.
Comments
Post a Comment