Main menu

Pages

SIRRUKAN DAKE TATTARE DA GERO A BINCIKEN GARGAJIYA DA KIMIYYA

 



Amfanin Gero da sirrikan da yake kumshe dasu a gargajiyance da Kuma kimiyyance.

Gero wanda a Turance ake kira da suna Millet, nau’in abinci ne daga cikin tsarin abincin da Allah (S.W.T) ya huwacewa kasar Hausa. Abinci ne mai tarin albarka da ke tattare da hikimomi na daban fiye dana sauran abinci. 



Wasu na daukar gero tamkar abincin talaka ko abincin mutanan kauye wanda hakan ya sa wani sai ya shafe fiye da shekara bai ci gero ba. Da dama muna tinanin ai shinkafa tafi dukkan sauran abinci muhimmanci, watakila ganin launin nata da kuma dandanon da ke gare ta. Sai dai kuma launin abinci ko dandanonsa ba shi ke fayyace muhimman sinadiransa ko amfaninsa a jiki ba. 



A lokuta da dama za ka ci abinci sai ka ji baya da dandano amma kuma yana amfanar jiki. Saboda yana gina jiki da yake kumshe da sinadarai. Haka kuma za ka iya cin abinci amma sai ya kasance dandanon ne kawai a tare da shi baya da wani sinadaran gina jiki a tare da shi. Duk da yake gero na daga cikin abinci naui’n carbohydrate amma yana da wata fa’ida ta daban da ta sha banban da sauran abinci.




 Ga kadan daga cikinsu.

- Ana abinci da gero, misalin tuwon gero.

- Ana yin fura da gero.

- Ana yin kunu ko koko da gero.

- Ana masa da gero.

- Ana yin gumba da gero.

- Ana yin dambu da gero.


Kusan gero ne kadai ake iya sarrafawa a haka sabanin sauran dangin abinci. A baya ga haka kusan kashi 70 na maganin gargajiya za ka cimma ana sha da kunu ko hura ta gero wanda idan aka sha to zai fi karfin aiki da kuma warkarwa ga abin da ake bukata.



Binciken kimiyya akan geto da abubuwan da ya kumsa

Ita kuma kimiyya tayi nata hubbasa wajen zakulo wa da muhimmancin gero da kuma maganin cututtukan da ya ke yi.


Gero na kumshe da sinadiran calcium, copper, iron, magnesium, manganese, selenium, potassium, phosphorus da kuma bitamins kamar su niacin, riboflabin, pantothenic, folate, folic acid, bit B6,bit C, bit E.


- Gero na samar da karfin kashin jiki dana kakora.

- Gero na rage tumbi da kiba ga musu jiki.

- Gero na dai-daita sinadiran cholesterol wadanda yawan su a jiki kan haifar da cututtuka ga zuciya da wasu matsaloli na daban.


- Gero na kare afkuwar tarin asma da kuma ciwon daji waton cancer saboda yana daukeda wasu sinadirai masu suna pantothenic acid da kuercetin dake jare jiki daga kamuwa da cancer.


- Gero na wanke wasu sinadiran dake gurbata ciki, sabili da sinadirin da yake dauke da shi mai suna kuercetin da ke taimakon koda da hanta yin aiki yanda ya dace kuma yana wanke su daga wasu cututtuka.


- Gero musamman idan aka yi hura na taimakwa jiki dan samun natsuwa da hutu da kuma isasshen bacci. Dan haka masu fama da hawan jini sai su nemi fura mai dan sanyin da baya da illa sai su zanka sha, za a ga faida.


- Gero na kare jiki daga anemia a dalili da samuwar sinadirran folate da iron da folic acid da kuma copper wadanda dukkan su sukan taimakawa jiki dan samun wadataccen jini.


- Gero na huce kumburin ciki, musamman ga mai fama da yawan kumburin ciki ko yawan tusa. Sai ya zanka shan hura ya rage cin abinci haka.


- Gero na gyara ciki ya maida ciki mai koshin lafiya.


- Gero ya kasance abinci na farko da ake baiwa kananan yara musamman a sanda suke girma ko sanda aka yaye su, indan ake basu kamar kunu ko koko ko hura ba tare da wata matsala ta faru ba. Yana samar masu da karfin kashin jiki da hakora da kuma kiyaye lafiyar cikinsu ba tare da gudawa ba.

Comments