Matsayin Mace Mai kaushin kafa, da Kuma hanyoyi Shida da za a bi don kawar da kaushin.
Akwai wani abu da masana suka aminta dashi shine Mace me dumin jiki musamman hannaye da kafafu ana samunta da danshi ajikinta, (ni'ima) atakaice mawuyacin al'amarine asamu mace irin wannan ta zauna batada ni'ima ko kuma tana yawan bushewa, da akwai wani masanin halayyar dan adam wanda ke zaune a kasar sudan wato (mursi al'bhagdi)
Yayi magana akan kaushi nau'ine na bushewar jiki wanda hakan yana hana ruwa bubbugowa daga jikin dan adam fiye da wanda bashi dashi, wannan hujjace babba da take nuna namiji zaifi bukatar mace me danshi a kafafu hannaye da dumin jiki,
Kowacce mace tanada ni'ima sai dai yanayin shan maganin mata ya banbanta kalar ni'imarta, saidai wata kuma tanada karancin ni'ima sai tanashan magani zata samu, dan haka a takaice idan kinada halitta me kaushin hannu da kafa kina jarraba magungunan laushin kafa da hannu,
Hanyoyi 6 da akebi don samun laushin kafafu da hannaye
(1) Khal Tuffa
Ana tafasa ruwan sai azuba masa man zaitun ana wanke kafa dashi,
(2) Man Ridi
Ana shafawa kafin a kwanta da safe awanke da ruwan dumi,
(3) Man Kadanya
Shi kuma sai an narkashi a zuba man zaitun aciki ana shafawa,
(4) Ayaba
Ayaba ana markada bawon asamu leda a saka kamar meyin kunshi idan ya kwana acire a wanke,
(5) Zuma
Ana amfani da sakar zuma kafin a kwanta a goga da safe a wanke da ruwan dumi,
(6) Albasa
Zaki raba jar albasa gida biyu saiki samu wani kyalle ko leda ki daure Rabin albasan a wajen wannan ruwan jiki Yana taba wajen ki barshi yayi kamar sa'o,i uku saiki cire ki wanke da ruwan dumi.
Comments
Post a Comment