Yanda Ake Miyar Ridi Musamman ga wannan watan na ramadan
Abubuwan da za a bukata
-Tattasai
-Albasa
-Attaruhu
-Ganye (Alayyahu ko Ugu)
-Nama da kifi
-Crayfish
-Manja
-Kayan kamshi
-Gishiri da maggi
Yanda za ki hada;
-Ki tafasa namanki ki tsame ki soya ki aje ruwan a gefe. Kifinki ma ki gyara ki dafa
-A zuba manja cikin tukunya ki kawo markadadden kayan miyarki wato attarugu, tattasai, albasa da kuma crayfish ki zuba a ciki ki soya sama sama
-Sai ki dauko ruwan tafashen ki zuba a ciki sannan ki zuba maggi da gishiri da kayan kamshi ki rufe ki barsa ya tafasa
-Sai ki dauko garin nikakken ridi wanda aka riga aka niko ta a injin nikan agushi ki yanka albasa ki yayyafa ruwa a ta murzata har sai ta kame tadan fara fitar da mai, sai a bude tukunyan ruwan miyan sai a zuba wannan ridin a cikinta
-Idan ya nuna sai ki kawo ganyen alayyahunki ko Ugu da kika wanke ki zuba ki barsa minti biyu ki sauke
-Zaa iya ci da tuwon shinkafa, sakwara ko semovita da duk wani nauin tuwo
Comments
Post a Comment