Ingantaccen Hadin Matan Aure hadu na musamman.
Abubuwan da za a nema
- Kankana
- Garin Kunun Aya
- Madara peak
- Zuma (optional)
Da farko zaki samu kankanarki mai kyau, in kwallo ne ki wanke bayan kafin ki yanka,in rabi zaki sa in duka ne duk dai yadda kike so, sai ki yanyanka ta kar ki cire kwalkayen duk dasu za ki hada.
Ki dauko blender dinki ki zubar a ciki kiyi blending. Sai ki kawo Garin Kunun Aya da yaji hadin (Aya, dabino, kwakwa, Kanumfari,) ki zuba a ciki, ki zubar madarar ki ta ruwa ko ta gari duk wadda kika samu.
Sai ki zuba a cup ki Sha, ke da kanki za ki fahimci wane irin aiki hadin yayi miki, ba sai na tsaya dogon bayani ba.
Comments
Post a Comment