Main menu

Pages

HANYA MAFI SAIKI DA ZAKI GANE WANE IRIN SKIN TYOE KIKE DA SHI

 


Yanda za ki gane kalar fatar ki, wato skin type, cikin sauki a cikin gidanki.


Aslm. Ina kuke ne Matan kwalusa, Ina wadda ta gaji da kashe kudin wajen siyen Maiko sabulu ta Yi ta asarar kudinka saboda in kinyi amfani da man ko sabulun baya karbarki.




Ke kenan kullum cikin canza Mai ko sabulu. To ga hanya magi sauki da za ki bi don ki gane skin type dinki, da zaran kin gane skin type naki to fa kin daina asaran kudinki wajen siyen kayan make up da ba su karbarki.




Da farko za ki samu simple face wash Wanda ba ya dauke da kowane irin chemical, idan ba ki da wannan ko zai maki wuyar samu to ki samu baby soap. Wato sabulun jarirai, irin su cusson, ko pears da sauransu 




Idan kika samu baby soap din sai ki wanke fuskarki da soap din ki barta kar ki shafa komai tsawon awa daya, idan skin dinki dry skin ne Zaki ki fuskarki ta bushe har ta na daddaurewa, idan normal skin ne Zaki ki fuskarki normal.




Idan Kuma oily skin gareki to Zaki ga fuskarki tayi Maiko sosai, idan Kuma combination skin gareki to za kiga daga saman goshi zuwa kan hanci da kasan baki wato haba, Zaki ga yayi Maiko gefen fuskanki Kuma kan kumatu da can gefe za ki ganta normal.



To Hakan na nufin kina da combination skin type. Duk wadda ta San skin type dinta to ta yi rabi na bangaren gyaran data ko jiki, don da sanin skin type ne za ki nemi Mai Wanda ya dace da skin type dinki. Don haka kowace mace tayi kokari tasan skin type dinta. Ma'assalam.


You are now in the first article

Comments