Main menu

Pages

YANDA ZAKI HADIN TSUMIN CREAMY MILK TABAJE

 


Yandà Ake Hadin Tsumin Creamy Milk Tabaje.


Abubuwan da za a a bukata;

- Sassaken Mangwaro
- Sassaken Sanya
- Kimba
- Citta
- Kanumfari
- Minannas
- Mazarkwaila ko sugar lump


Da farko zaki wanke sassaken mangwaronki sosai sai ki Saka a turmi ki ta dakawa, in kina dakawa za ki ga madarar na fitowa, ki daka ya daku sosai. 




Sassaken Sanya da sauran ingredients din duk Suma zaki zuba su cikin turmin ki hade da sassaken mangwaron ki ta dakawa su damu.



Daman kin tafasa ruwanki sai ki zubar wadannan abubuwan da kka dauka a ciki kisa hannu kira murzawa har kiga ruwan ya koma kalar milk, sai ki tace ki zubar sugar lam ko Mazarkwaila shinan sai Sha 



Zai saukar miki da ni'ima sosai da sosai sannan Kuma duk wani sanyi da ke jikinki zai magance shi Insha Allah. Shawara a matsayinki na Mace ki kokari ki kauce ma shaye - shayen kayan Mata batkatai da cushe - cushen da ba kusan da me aka hada su ba.




Ki tsaya a kan abubuwan da Zaki hada da hannunki, kika San tsaftarsu da ingancin su Kuma ba tare da kashe kudade masu yawa ba. Wannan shawara ce kawai Wanda yaga zai iya dauka to Alhmdlillh.




Comments