Kina so Farcen hannunki da na kadai sunyi haske sunyi kyau sannan kina son magance Kaushi ko faso a kafarki, ga yadda Zaki;
Assalamu alaikum. Da farko Zaki samu container karama ki zuba gishiri cokali biyu, toothpaste wato man goge baki kowane iri cokali daya, man kwakwa cokali daya sai ki kwaba sosai.
Idan ya kwabu sai kike shafawa a saman farcenci, bayan minti goma ki wanke, cikin satin daya za ki ga yadda farcenki zai yi kyau. Sannan kuma idan kina son cire duk wani kaushi ko kaujen dake kafarki sai ki hada wannan.
Gishiri cokali biyu, toothpaste cokali daya man kwakwa cokali daya sai nourishment oil da kike amfani da shi cokali daya ki motse, kie shafawa a tafin kafarki. Ki jure yin haka kullum za ki ga sakamako Mai kyau Insha Allah kafarki za tayi kyau sosai.
Comments
Post a Comment