Ingantaccen Hadin Matan Maiduguri, da Kasaitattun Mata kadai suka san shi.
Aslm. Wannan hadi ne mai sauki wanda Matan Maiduguri su keyi a maidugurin ma sai kasaitacciyar mace ne tasan da shi.
Shiyasa naga ya dace na kawo maku don ku amdana.
Hadi ne Mai sauki da saukin gudanarwa, da farko Zaki samu Dabino da garin Habba, (Habbatus -Saudah). Kullum dare kafin ki kwanta sai ki dauki dabino guda uku, ki bare cikinsa ki cire kwallon.
Sai ki debi Garin Habba din da yatsunki ki zuba cikin dabinon sai ki cinye, haka Zaki ma duka uku. Da safe ma kafin kici komai kici wannan hadin, da kanki za ki gane tasirin sa a jikinki Insha Allah.
Comments
Post a Comment