Yanda za ki hada man shafawa Mai kyau don gyaran fata tayi haske Mai kyau da taushi.
Assalamu alaikum. Ina Matan suke, ga Lokacin sanyi ya shigo ki zo ki koyi yadda za ki hada Mai mai kyau da gyara miki fata, tayi taushi da laushi da sheki.
Da farko za samu karas, sai ki gogashi a magogi, bayan kin gama gurza shi, sai ki dauki oil wanda kike amfani da shi, sai ki zuba cikin gogaggen Karas din ki.
Daga nan sai ki dora Ruwa a tukunya idan yayi zafi sai ki dora karas din dake hade da man, in turirin ya ratsa shi sosai sai ki dauke ki tace man. Sai ki dauki aloe vera gel din da kika cire daga jikin alovera din ki zuba man karas din nan kiyi ta juyawa sosai har ya hade jikinsa za ki ganshi yayi kamar cream.
Shkenan sai kike shafawa za kiga yanda jikinki zai yi kyau sosai musamman yanzu da sanyin nan ke busar da fata.
Comments
Post a Comment